Gwamnan Zulum Zai Gina Hanyoyi Masu Nisan Kilomita 316 A Jihar Borno

zulum (16)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Zulum zai gina hanyoyi masu nisan kilomita 316 wanda ya hadu da manyan garuwa dama wadanda ke makotaka da kamaru da Nijar.

Garuruwa 6 da zasu hadu sun hada da Monguno, Ngala, Bama, Damboa, Biu, Askira, da Chibok.

Acewarsa yankunan Banki, Gambouru da Dikwa na cikin garuruwan da ked a iyaka da kamaru.

Gwamna Zulum ya bayyana hakan a kwanakin nan a Maiduguri yayin mika kasafin shekarar 2021 na naira biliyan 208.7 ga majalisar jihar.

Yace ma’aikatar ayyuka da hukumar gyaran hanyoyi ta jihar Borno ne zasu fara aikin gyaran hanyoyin a shekara mai zuwa.

Haka nan yace an ware naira biliyan 11.8 da naira biliyan 7.5 billion don gudanar da wasu ayyukan.

San nan yace akwai shirin dake kasa da gidauniyar Dangote don fara aikin hanyar Bama zuwa banki mai nisan kilomita 65km sai kuma mai nisan kilomita 55 daga titin Dikwa zuwa Gambouru a shekarar 2021.

Yace suna da niyyar bude titunan dake da iyaka da Dikwa, Gambouru, Bama da Banki daga watan Mayu na shekarar 2021 koma kafin nan.

San nan ya tabbatarwa da jama’a cewa gama ayyukan hanyoyin zai sa mutane su dinga zuwa suna komawa ba tare da takura ba wanda ya hada kimanin garuruwa 10 ciki harda wadanda ke bakin iyaka da kasar.

Haka nan yace za’a gyara garuruwan Benisheikh, Askira da Monguno ciki harda aikin titin Maiduguri zuwa Bama.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply