Gwamnan Zulum Tare Da Jami’an Jin Kai Sun Isa Jamhuriyyar Kamaru Da Batun Dawo Da Yan Najeriya 9,800 Gida

zulum (16)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum tare da sauran jami’an gwamnatin tarayya na ma’aikatar al’amura da walalan jama’a na tarayya sun isa Marwa na jahuriyyar kamaru cikin ayyukan jin kai na dawowa da yan Najeriya 9,800.

Kimanin yan Najeriya 46,000 da suke mafaka sansanin Minawao na Kamarun yan jihar Borno ne ciki mutane 9,800 ne suka amince u dawo karkashin kashi na fari da zasu zauna a gidaje da gwamna Zulum ya gina a garuruwan Bama da Banki.

Gwamna Zulum ya jagoranci ayarin zuwa kasar Kamarun a yammacin talata domin halartar taro kan yerjejeniya tsakanin Najeriya da Kamaru na dawowa da jama’an gida wanda wakilan majalisar dinkin duniya zasu halatta a Marwa.

Kafiyan tafiyar nasa zuwa Kamaru, gwamna Zulum yasha tattaunawa tare da ministan kasashen waje Geoffrey Onyeama da ministan al’amuran jin kai da walwala Hajiya Sadiya Farouq, sai kuma hukumar matafiya dayan gudun hijira hade dai jakadai da sauran su duk a kokarin dawowa da jama’a.

Gwamna Babagana Umara hade da sakataren ma’aikatar jin kai Malam Bashir Nura Alkali da kuma daraktan ma’aikatar, Ali Grema ne suka isa kasar na kamaru harma da sauran mukarrabai daga hukumar matsugunai da gudun hijira.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Related stories

Leave a Reply