Gwamnan Kebbi Ya Amince Da Sabon Dokar Hukuncin Kisa Ga Duk Wanda Aka Kama Da Laifin Garkuwa Da Mutane A Jihar.

kebbi
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya amince da sabon dokar na wannan shekara na hukuncin kisan kai ga duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane a jihar.

Wannan dokar wanda ya kasance cikin dokoki 5 da gwamnatin jihar ta amince, haka kuma tace duk wanda aka kama da laifin fyade hukuncin sa zama a gidan kaso na har abada.

Sanarwar wanda attoney janar kuma kwamishiniyar shari’a na jihar Rahmatu Adamu Gulma ta sanyawa hannu.

Ta cigaba da cewa dokar da aka shimfida na wannan shekarar, hukuncin garkuwa da mutuum karkashin sashi na dari 2 da 47 na dokar shine kisa sai kuma hukuncin fyade karkashin sashi na dari 2 da 59 shine hukuncin zama a gidan kasa na har abada.

Ta kara dacewa wannan doka zai sa a samu raguwa wajen cunkoso a gidan yari
Haka kuma gwamnan ya amince da dokar samar da kwalejin lafiya da fasaha a Jega da kuma sake dokar lamba na 5 na shekarar dubu 1 da dari 9 da 9 da 3 na samar da kwalejin ilimi na Adamu Augie dake Argungu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply