Gwamnan Jihar Yobe Ya Amince Da Aiwatar Da Rahoton Kwamiti Na Sake Farfado Da ilimin Bai Daya A Jihar.

yobe2
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya amince da aiwatar da rahoton kwamiti kan sake farfado da ilimin bai daya dana sakandare a jihar.

Wannan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da darakta janar na yada labarai ga gwamnan Mamman Muhammad.

Sanarwar tace gwamnan Buni ya sanay dokar ta baci yayin hawan sa mulki a bangaren ilimi na bai daya dana sakandare domin inganta cibiyar ilimi na jihar.

Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin farfaesa Malah Daura mataimakin chansilo na jami’ar jihar Yobe tare da wasu manya a bangaren ilimi a matsayin mambobi domin inganta tsarin shirin.

Gwamnan yace bangaren ilimi yana da muhimmanci a gwamnatin sa kuma zaiyi iya kokarin sa domin inganta bangaren.
Mai bada shawara na musamman ga gwamnan kan harkar ilimi Dr. Kole Shettima kuma mamba a kwamtin ya yabawa gwamnan.

Haka kuma kwamitin ta bada shawara kan doka mai karfi domin kula da ayyukan da tabbatar da shi.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply