Gwamnan Jihar Taraba Yayi Alkawari cika Duk Alkawarin Da Ya Dauka .

taraba
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku ya tabbatarwa kungiyar tsoffin rundunar soji rashen jihar cewa zai cika musu duk alkawuran su.

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin bikin tunawa da mazan jiya da aka gudanar a Jalingo.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakin sa Haruna Manu, gwamnan yace sadaukarwar da jami’an soji sukayi ba zai taba misaltuwa ba.

Yace gwamnatin sa tana kokarin a kullum wajen kyautatawa tsoffin sojin domin jin dadin rayuwar su.

Yayi kira ga jama’ar jihar da su goyon baya ga kokarin mazan jiya wajen taimaka wadan da suke aiki a yanzu.

Shugaban kungiyar tsoffin soji na jihar Taraba Alh Sa’idu Muhammad yayi anfani da wannan dama wajen neman bukata ga gwamnan da ya kara yawan lambar tsoffin jami’an na kirista da musulmai domin ziyartar kasar Isra’ela da Saudiya.

Daga karshe kakakin majalisar dokoki na jihar Taraba Dr. Joseph Albasu Kunini ya yaba da kokarin jami’an sojojin wajen kokarin su ga kalubalen da ake fuskanta na tsaro a kasar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply