Gwamnan Jihar Nasawara, Yace Ya Kamata Shugaba Buhari Ya Hayo Sojojin Chadi Domin Fatattakar Mayakan Boko Haram A Yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya.

NASARAWA STATE
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Nasawara, Abdullahi Sule, ya ce ya kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya hada kai da sojojin Chadi idan yana son fatattakar mayakan Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Sule ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai
Idan za a iya tunawa gwamnan Nasarawa wanda ya ziyarci jihar ta Borno bayan kashe manoma shinkafa sama da 40 da kungiyar Boko Haram ta yi,

ya ce ya kamata a binciki wasu hanyoyin domin kawo karshen tashe tashen hankula a Arewa-maso-Gabas.

koda yake , ya yabawa Shugaban kasar kan namijin kokari da yake game da matsalar rashin tsaro a kasar.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya kuma roki Shugaba Buhari da ya hayo sojojin ko neman taimakon sojojin kasashe kamar Chadi, Kamaru, da sauransu domin fatattakar ‘yan ta’addan Boko Haram.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply