Gwamnan jihar Gombe Ya Dakatar Da Wasu Ma’aikata .

Akalla ma’aikata dari 6 da 68 ne aka dakatar daga aiki bayan fara bincike da akayi.

Kwamishinan kudi da cigaban tattalin arziki na jihar Muhammad Magaji shi ya bayyana haka a wajen taro a jihar.
Kwamishinana yace ma’aikatan da abin ya shafa sune wadanda basu zo tantancewa ba bayan fara rajista saboda haka aka dakatar da su.

Ya kara dacewa ma’aikata dari 4 da 31 daga ma’aikatu 84 da hukumomi da sassa da dama ne abin ya shafa.

Yace anyi wannan tsarin ne a kananan hukumomi 2 na Gpmbe da Akko.

A cewar sa adadin ma’aikata dari 1 da 3 ne na karamar hukumar Gombe basu kasnace a cikin binciken ba da ya hada da ma’aikatan kananan hukumomi 44.

A karamar hukumar Akko kuma ma’aikata dari 1 da 34 ne abin ya shafa daya hada da ma’aikata 83.

Kwamishinan yace an samu kudade na sama da naira miliyan 31 da miliyan 3 da . 19 a kananan hukumomin 2.

Yace adadin ma’aikatan na kananan hukumomin 2 sun kai dubu 67.