Gwamnan Jihar Borno Ya Yaba Da Sadaukarwar Dakarun Tsaro A Yakin Da Suke Da Yan Boko haram

zulum (16)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar borno ya yaba kokari da sadaukarwa da dakarun tsaro da sauran ma’aikatun tsaro sukeyi wajen yaki da yan boko haram da kuma kalubale da dama dasuka shafi jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan yayin dayake jawabi a taron tunawa da sojoji da’aka gabatar a Ramat square , Maiduguri.

Gwamnan ya samu wakilcin mataimakin sa Umar Kadafur, wanda yace ranar ta tunawa da sojoji ta cancanci tunawa ga gwamnatin jihar da kuma al’ummar jihar saboda irin sadaukarwa da sukayi wajen kokarin magance matsalar ta boko haram a jihar dakuma arewa maso gabacin najeriya.

Yace murnar ta fara tun 9th zuwa 15th na watan janairu domin yin adu’a ga wadanda aka rasa dakuma manyan jarumai.

A bayanin sa yace an samu hallatar shugaban tsaffin sojoji na reshan jihar borno, captain William Manza inda ya yabawa gwamnan da gwamnatin ta jihar, rundanar tsaro shi’a ta bakwai dake babban birnin Maiduguri a kasar Najeriya, majjalissar jihar borno, alkalin alkalai dakuma sauran manya da suka hallata.

An samu jimlar naira miliyan 15, inda gwamnan jihar farfesa babagana umara zulum ya bada naira miliyan 10 da sauran taimako daga wadanda suka hallata.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply