Gwamnan Jihar Bauchi Ya Yaba Da Kokarin Kwamitin Rabon Kayan Tallafin Covid 19.

bauchi_governor
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad na jihar Bauchi ya yabawa mambobin kwamitin rabon kayan tallafi na covid 19 a jihar wajen rabon kayakin da sukayi yadda ya dace.

Gwamnan yayi wannan yabon ne lokacin rabon kayan tallafin karo na karshe ga mazauna karamar hukumar Bauchi.

Yace dukkan kayan tallafin an raba su ga wadanda akayi domin su haka kuma babu wani mutun ko kungiyar da ta karkatar da kayan zuwa wani wajen.

Yace kowani gida daya ya samu buhun shinkafa mai nauyin kilogram 10 dana masara mai nauyin kilogram 10 dama hatsi mai nauyin kilogram 5 da wake ma mai nauyin kilogram, da buhun siga mai nauyin kilogram 2 da taliya leda 3 da sinadarin dandano dari 1 da gishiri kilogram 1 da man girki da man ja lita 2.

Yace kwamitin rabon kayan tallafin ta raba abinci kimanin dubu dari 1 da 10 ga kananan hukumomi 20 na jihar domin saukakawa mutane radadin da suke ciki sakamakon bullar cutar corona.

A nasu jawabi mataimakin gwamnan jihar kuma shugaban kwamiti kan cutar corona sanata Baba Tela da mai martaba sarkin Bauchi kuma shugaban kwamitin rabon kayan tallafi sun bayyana godiyar su ga gwamna Bala da bai sanya kanshi cikin al’amuran kwamitin ba.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply