Gwamnan Jihar Bauchi Ya Raba Motoci 154

Bala-Mohammed-new
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Muhammad ya kaddamar da rabon keke napep dari 6 da 55 da kuma motoci dari 1 da 54 domin karfafa tsarin sufuri a jihar.

Yayin kadamar da rabon abubuwan hawan, gwamnan yace hakan na daga cikin kokarin gwamnatin sa na bada dama ga jama’ar jihar sa wajen dogara da kansu.

An kaddamar da abubuwan hawan karkashin shirin Kaura Economic Empowerment Programme wanda ake mai lakabi da KEEP 2020.

Gwamnan ya kara dacewa shiri karo na 3 zai maida hankali ne kan motocin dake diban kaya gay an kasuwa da babu kudin ruwa a ciki.

Kakakin majalisar dokoki na jihar Bauchi Abubakar Y Sulaiman da shugaban jam’iyyar PDP Alh. Hamza Koshe Akuyam sun yabawa gwamnan na cika mafi yawan alkawuran da ya dauka yayin yakin neman zabe musamman ma a bangaren karfafawa jama’a.

A nashi bangaren kwamishinan habbaka kanana da matsakaitan masana’antu Alh. Modibbo Ahmed ya yi godiya ga gwamnan na taimakawa ma’aikatar sa wajen kawo abubuwan karfafawa jama’a domin rage ta radadin talauci.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Related stories

Leave a Reply