Gwamnan Fintiri Ya Umarci Masu Gidajen Shagulgula Da Su Rika Rufewa Karfe Goma Na Dare Domin Hana Yaduwar Corana

fintirii
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya umarci masu gidajen shagalgalu da su rika rufewa karfe goma na dare domin hana yaduwar annobar ta corana virus, kamar yadda gwamnati take iya kokarin ta waje hana yaduwar cutar.

Ya kuma gargadi mutanan jihar dasu rika amfani da takunkumin fuska, kiyaye shiga cikin taro, yawaita wanke hannaye dakuma amfani da man wanke hannu tareda rage tafiye-tafiye idan bai zama dole ba.

A bayanin mai magana da yawun gwamnan Humwashi Wonosikou, yace gwamnatin na kokari wajen hana yaduwar cutar dukda masana fannin lafiya sunce tafi ta farko sauri wajen bazuwa, dan haka gwamnatin zata dauki matakai wajen hana yaduwar cutar.

Gwamnan ya tabbatar da cewar za’a bar harkokin kasuwanci su cigaba domin babu wanda yakeso ya sake kasancewa acikin tsaro kamar yadda ya gudana a baya amma da sake bada shawarar mutanan jihar suyi kokari wajen amfani da dukkan wani hanya daya dace wajen hana bazuwar cutar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply