Gwamnan Buni Ya Kashe Naira Billiyan Biyar Domin Gyara Ma’aikatar Kiwon Lafiya A Jihar Yobe .

yobe mai mala
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya kashe naira billiyan biyar domin gyara manya da kananan ma’aikatar kiwon lafiya cikin unguwanni dari da saba’in da takwas daga farkon shekarrar 2020 ta zuwa karshen ta.

Haka zalika Gwamnatin sa ta gama shirinta na daukan malaman makaranta dubu uku a cikin wannan shekara ta 2021 tare da kuma shirin farfado da makarantan Almajirai mussamman wadan da suke karatu a wasu jihohi da aka dawo dasu gida sakamakon bullar cutar COVID-19.

Kwamishinan harkokin gida da yada labarai Abdullahi Bego shine ya bayyana hakkan a yayin da suke taron sun a karshen shekara a damaturu babban birnin jihar.
Ya kara da cewa cikin billiyan biyar din a gina sabon bangaren kula da mata da kuma jarirai a asibitin koyarwa dake damaturu tare da gyara kanannan asibitoci dake kannanan hukumomi machine da yusufari da kuma da wasu gyarraraki da akayi a asibitoci cikin kanannan hukumomi goma sha bakwai a cikin jihar.

Bego ya kara da cewa an gina wasu gidajen likitoci talatin da tara a kwatas dinsu,bada magunguna kyauta ga wadanda bam ya shafa tare da Karin kudi ga dalibai masu karatu a bangaren kiwon lafiya da dai sauransu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply