Gwamna Zulum Yayi Kira Ga Gwamnatin Tarayya Da Ta Wadata Hukumar Tsaron Civil Defence Da Kayakin Aiki Domin Su Yaki Yan Ta’adda.

zulum (16)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamna Babagana Umara Zulum ya bukaci gwamnatin tarayya da ta wadata hukumar tsaron farin kaya na civil defence a jihar nan da sauran shiyoyi a yankin arewa maso gabas da kayakin aiki da zai taimaka musu wajen yaki day an ta’addan BH da kuma sauran ayyukan ta’addanci.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin taron da aka gudanar a shalkwatan hukumar a nan Maiduguri, gwamna Zulum ya kara dacewa tun bayan kafa hukumar tana iya kokarin ta wajen gudanar da ayyukan ta.

Gwamna Zulum ya bukaci kwamanda janar an hukumar Alh. Abdullahi Gana Muhammadu da a tura yan asalin jihar nan wajen taimakawa a daidaita tsaro a jihar nan yayin day an gudun hijira ke komawa garurun su na asali.

Kwamanda janar na hukumar Abdullahi Gana Muhammadu ya yabawa gwamna Zulum da irin cigaba da bada goyon baya da yake ga hukumar musamman ma ga masu kula da tsaron manoma.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply