Gwamna Zulum Yaraba Kayan Abinci Ga Yan Gudun Hijira Dubu 10 A Damasak.

zulum (16)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Yayin kwanan sa na 2 a garin Damasak, a ranar Lahadi gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum ya duba rabon kayakin abinci ga yan gudun hijira dubu 10 dake cikin bukata.

Kowani iyali na mutane dubu 10 sun samu buhun shinkafa mai nauyin kilogram 25 da wake, masara, da lita 5 na man girki domin saukaka musu rayuwa a garin na Damasak.

Damasak shalkwatan karamar hukumar Mobbar dake arewacin jihar Borno a baya ya kasance a hannun yan ta’addan Boko Haram kafin daga baya aka karbe kuma gwamnan Zulum ya sake matsugunai ga jama’ar garin.

Haka kuma gwamnan yayi rabon kayakin ban ruwa, da taki, da irin shuka da sinadarai da kuma naira dubu 5 ga manoman ban ruwa su dubu 1 da dari 2 da suka fara noman rani.

Gwamnan ya samu rakiyan sanatan dake wakiltar mazabar Borno ta arewa sanata Abubakar Kyari wanda kuma dan asalin Damasak ne sai kuma shugaban rikon kwarya na jam’iyyar APC Ali Bukar Dalori, kwamishinan noma injiniya Bukar Talba da wasu masu ruwa da tsaki dake da hadi da karamar hukumar Mobbar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply