Gwamna Zulum Yakai Ziyara Babbar Hanyar Maiduguri zuwa Damaturu

ZULUM
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci garin Jakana, daya daga cikin manyan yankunan da ke kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, a lokacin da ya nuna fushinsa kan hare-hare da ke afkuwa akan matafiya da mazauna kauyukan da’ yan Boko Haram ke kaiwa

Zulum ya ce abin takaici ne yadda ake kai hare-haren a cikin shekaru biyu da suka gabata, tsakanin Auno da Jakana, mai tazarar kilomita 20.

Haka zalika Gwamnan ya ce ya yi bakin ciki matuka duk da goyon bayan da suke samu daga Gwamnatin Tarayya da ta Jiha, amma sojoji sun kasa kawo tsaro a yanki mai nisan kilomita 20, Auno da Jakana.

Hailayau Gwamnan ya ce lokacin da ya yi tafiya tare da manema labarai daga Maiduguri zuwa Jakana. Ba su ga sojoji a kan hanya ba, hatta masu kawo dauki a kan hanyar basa nan .
Gomnan ya kara da cewa a wannan shekarar kadai, maharan sun kai hare-hare da dama a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu ciki har da wanda aka yi a watan Fabrairun, inda sama da mutane 30 ciki har da wata mata mai shayar da jariri da suka kone kurmus a hanyar

Gwamna Zulum ya tabbatarwa mazauna kan titin cewa zai gudanar da taron tsaro nan take sannan kuma zai tsamar da matakan tsaro a kan babbar hanyar.

Gwamnan yayi kira ga ‘yan kasar da su gigaba da bayar da rahoto duk wani abun da basu aminta da shiba ga jamian tsaro domin kawo karshen tashe tashen hankula a kasar .

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply