Gwamna Zulum Yace Wadanda Aka Sauya Musu Tunani Su Sake Komawa Kungiyar Boko Haram.

zulum (16)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum yace shirin sauya tunanin yan Boko Haram da aka shirya tun farko ba kamar yadda ake tunani bane.

Gwamnan ya bayyana haka a wajen taron kungiyar gwamnonin arewa maso gabas da aka gudanar a ranar Laraba a dakin taro dake gidan gwamnati a jihar Bauchi.

Gwamnonin da suka halarci taron akwai gwamnan jihar Borno, Adamawa, Gombe da kuma Bauchi sai kuma gwamnonin jihohin Taraba dana Yobe mataimakan su ne suka wakilce su.

Gwamnan Zulum yace wadanda aka sauyawa tunani ma sun sake komawa aikin ta’addan ci bayan sun gane sirrin jama’a.

Yace hanya mafi dacewa shi ne kawar da yan ta’addan da ayyukan ta’addancin su, yace wadanda aka sanya su dole a cikin ta’addancin kuma aka ceto su ko suka kubuta sune ya kamata a sauya musu tunani.

Daga karshe gwamnan ya bayyana jingirin da aka samu wajen daukan mataki kan yan ta’adda, ya bukaci attoney janar na tarayya da ya bari a dauki matakin hukunci.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply