Gwamna Zulum yace tare da taimakon yan banga a yanzu Maiduguri yafi birnin tarayya ingancin tsaro.

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum yace yana amfani da yan banga wajen magance matsalar rashin tsaro a jihar sa.

Gwamnan ya bayyana haka a Owerri yayin da ya samu wasikar gayyata na bada lambar yabo daga kungiyar yan jaridu ta kasa reshen jihar Imo.

Gwamna Zulum wanda ya samu wakilcin babban mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai Baba Sheikh Haruna yace yan bangar na daga cikin kokarin gwamnatin Zulum domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

A cewar sa jihar Borno yana fuskantar matsalar tsaro tun shekaru 12 amma duk da haka ana samun sauye sauye da dama.
Daga karshe yace idan aka zo Maiduguri ya ma fi birnin tarayya kwanciyar hankali ba kamar yadda ake yadawa a waje ba.