Gwamna Zulum Yaba Da Sanarwa Zaa Bayar Da Naira Biliyan 12 Domin Biyan Gratuti

Zulum
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Barno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ba da sanarwar bayar da naira biliyan 12 domin biyan masu gratuti 4,862 da suka bar aikin kananan hukumomi daga shekarar 2013 zuwa 2017.

Zulum ya bayar da naira biliyan 3 a watannin Yuni da Satumba 2019, domin biyar ‘yan fansho 1,684 da suka bar aikin gwamnati daga 2013 zuwa 2019.

Gwamna Zulum ya kaddamar da biyan ne tare da gabatar da cheques kudi ga wasu masu ritaya a gidan gwamnati dake Maiduguri.

Gomnan Ya bayyana cewa an samo, kudadin ne daga rancen da Bankin Zenith ya bayar.

Da yake jawabi kan batutuwan fansho, gwamnan ya bayyana cewa daga watan Mayu na shekarar 2019 zuwa yau, an karbi korafe-korafe guda 770 daga ciki harda na yan fanshon da ba a biyasu ba .

Zulum ya kuma kara da cewa a kwanan nan ne gwamnatin jihar ta kammala gyaran Sakatariyar Musa Usman, da samar da kayan daki. Gwamnan ya kuma ba da tabbacin jajircewar gwamnatin sa na cigaba da biyan kudaden yan fansho yadda ya kamata.

Wakilinmu ya ruwaito cewa biyan kudin penson ya kasance abu mai mai matukar wahala a duk fadin Najeriya ganin cewa, kudade ne da ake bayarwa a dunkule ga wayanda sukayi ritaya a matsayin ladan shekaru aikin da sukayiwa gomnati

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply