
Gwamnnan jihar Borno ferfesa Babagana Umara Zulum tare da jakadan kasar chadi Zannah Umar Bukar Kolo sun kai ziyara ga shugaba idriss Debby domin tattaunawa akan dawowa da yan gudun hijran jihar Borno gida.
Shuwagabanni biyun sunyi tattaunawar ne a fadar shugaban kasar dake N’Djamena tare da jakadan kasar najeriya, Mr Abakar Saleh Chahaimi.
Gwamna zulum a farkon shekaran ya gana da manyan sojoji na hadin gwuiwar kasa da kasa a kan yaki da ya kungiyar yan Boko haram.

Haka zalika gwamnan ya kai ziyara kasashen kamaru da nijar a lokuta da dama domin haduwa da yan gudun Hijira dake makobtaka da kasashen dake kan iyaka.
A duk lokacin da Gwamna Zullum ya kai irin wannan ziyaran yana sa ido akan bara kudade da kuma kayakin Abinci tare da mika godiyarsa ga gwamnati da kuma al’umma dake cikin kasashen.
