
A ranar Lahadi da daddare ne gwamna Babagana Umara Zulum ya ziyarci sansanin yan gudun hijira na kwalejin harkokin addinin musulunci na Muhammad Goni a Maiduguri inda yan gudun hijira daga karamar hukumar Abadam suke.
Da shigar sa sansanin gwamna Zulum ya rufe kofa domin dudduba al’amuran yan hijira da kuma sanin asalin an hijira da kuma yan gari da suke zama a sansanin domin samun kayakin tallafi da ake rabawa da sunan yan hijira.
Manufar gwamna Zulum wanda ya kare da misalin karfe 1 na safe, cikin bayanan jami’an aikin agaji cikin yan hijira dubu 1, dari 6 da 50 ba yan asalin hijira bane.
Asalin yan hijira dari 4 da 50 ne kawai aka gano yan hijira yayin ziyarar da gwamnan ya kai tare da jami’an hukumar bada agajin gaggawa na kasa air commodore MT Abdullahi da kwamishinonin noma da na kanana hukumomi da harkokin masarautu.
