Gwamna Zulum Ya Yaba Da Ziyarar Da Sabon Shehun Ya Kai Masa inda Yace Allah Ne Ya Zabe Shi.

ZULUM-INAUGURATE-COMIITE
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jiha Babagana Umara Zulum yayi kira ga sabon Shehun Dikwa, Ibrahim Ibn Umar Ibrahim Elkanemi da ya bada shugabanci mai kyau a masarautar tasa mai girma da albarka.

Gwamnan yayi kira yayin da sabon shehun da jama’arsa da masu ruwa da tsaki suka ziyarci gidan gwamnatin don gode masa kan nada shi da yayi a matsayin Shehun na Dikwa.

Shehu Ibrahim Ibn Umar Ibrahim Elkanemi ya karbi takardar sa a matsayin Shehun Dikwa na 13 bayan rasuwar marigayi Shehun Dikwa Muhammad Ibn Masta Elkanemi na biyu.

Gwamna Babagana Umara Zulum ya yaba da ziyarar da sabon Shehun ya kai masa inda ya bayyana shi a matsayin wanda ya dace da matsayin, inda yace Allah ne ya zabe shi.

Haka nan gwamnan ya bukaci sabon shehun da ya zauna a masarautar sa kuma ya taimakawa iyalan marigayi Shehun Dikwa da sauran ma’aikatan marigayi Shehun Dikwa.
San nan ya tabbatar wa sabon shehun taimakon gwamnatinsa don samun nasara wajen gudanar da mulkinsa dama samun tsaro a yankinsa.

Shehu Ibrahim Ibn Umar Ibrahim Elkanemi ya bayyana godiyarsa ga gwamna Zulum da nadin da yai masa inda ya broki Allah ya cigaba da kareshi.

Haka nan sarkin yayi alkawarin aiki daga yaankinsa dama taimakawa iyalan marigayi shehun na Dikwa dama gudanar da aiki da dukkanin ma’aikatan tsohon Shehun.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply