Gwamna Zulum Ya Ware Sama Da Naira Miliyan Dari 6 Domin Biyan Kudin Karatun Yara Na Scholarship.

zulum (16)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum ya ware naira miliyan dari 6 da 24 da digo 3 na karatun dalibai wato scholarship yan asalin jihar su dubu 23 da dari 7 da 76 a dukkan makarantun gaba da sakandare 49 dake fadin kasar Najeriya.

Kwamishinan manyan makarantu, kimiyya da fasaha da kuma kere kere, Dr. Babagana Mustapha Mallumbe shi ya bayyana haka a wata sanarwa, yace tuni aka fara biyan dalibai a manyan makarantu 9 da naira miliyan dari 3 da 20.

Kwamishinan ya bayyana wadanda aka basu kudin na scholarship da suka hada da daliban dake aji 4 da na aji 5 a jami’ar Maiduguri, da jami’ar jihar Borno, da Polytechnic na Ramat da kwalejin ilimi na Kashim Ibrahim, kwalejin ilimi na Waka Biu, kwalejin karatun addinin musulunci na Muhammad Goni, kwalejin ilimin kasuwanci dake Konduga, kwalejin ilimi, kimiyya da fasaha na Umar Ibn Ibrahim dake Bama sai kuma kwalejin noma na Muhammad Lawan.

Haka kuma kwamishinan ya bayyana cewa gwamnan ya amince da taimakon kudade ga likitoci yan asalin jihar Borno da suke da bangarori daban daban a kasar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply