
By: Hadiza Garba, Maiduguri
Gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum ya taya dukkan al’umma Krista a jihar dama Najeriya murnnar bikin kirsimeti kuma yayi fatan ayi cikin zaman lafiya da annashuwa.
Gwamnan ya bukaci yan Najeriya dasu dauki lokaci a wannan rana suyi tunani.
Yae jama’a su kula da wadanda suke sintiri tsakanin su dama kuma suyi waiwaye akan irin ayyukan da sojoji keyi da ma matasan tsaro na sa kai, maharba, da yan banga wandanda suke nasu bikin kirsimetin cikin jeji suna yakan yan ta’adda da kuma yadda nasu iyalan za suyi bikin babu su.

Kuma yace kamar kullum ya tabbata an biya albashin ko wani ma’aikaci kafin kirsimeti tare da bada duk wani gudumuwa da ake bukata don gudanar da bikin.
Cikin sakon kirsimetin daya mika, gwamnan yayi kira ga rundunnar tsaro cewa suci gaba da tsaya wa akan aikin da suke yiwa kasa da kuma alkawarin kare rayuka da dukiyoyin al’umma sannan yayi alkawarin karfafa su.
