Gwamna Zulum ya taimakawa hukumar sufiri ta Borno Express da motoci 90

ZULUM-INAUGURATE-COMIITE
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamna Babagana Umara Zulum a ranar juma’a yayi bikin bude motoci kirar Bus guda 90 don karfafa ayyukar hukumar sufuri ta jihar ta Borno Express wanda yake mallakar gwamnatin jihar.

Motocin sun hada da 40 masu kujeru 50 da kuma 50 masu kujeru 14 wanda gaba daya zasu dauki fasinjoji 2,740seaters inda aka agabatar da guda 70 sai 20 wadanda aka sani ne.

Zulum ya bayyana motocin a dandalin filin Ramat dake birnin Maiduguri yayin bikin wanda ma’aiktar sufuri ta jiharta shirya wadda ita take kula da ayyukan na Borno Express.

Gwamna Zulum ya umarci daraktan ma’aikatar ta sufuri day a hada hannu da ma’aikatar shari’a da sauran masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa an tsaftace harkar masu Keke Napep.

Kwamishinan sufuri na jihar Dr. Abubakar Tijjani ya tabbatar da cewa nan bada dadewa ba zasu rarraba motocin don amfanin jama’a.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Related stories

Leave a Reply