Gwamna Zulum Ya Sallami Kwamishinan Lafiya Na Jihar Borno

zulum (8)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya sallami kwamishinan lafiya na jiha Dr Salihu Kwayabura daga mukamin sa.

Mashawarcin gwamnan a al’amura hulda da jama’a Malam Isa Gusau ne ya sanar da hakan a yau a birnin Maiduguri tare da cewa hakan yana da cikin sake tsare-tsare a ma’aikatar.

Cikin sanarwar, gwamna Zulum ya godewa Dr Salihu Kwayabura da irin gudumuwa da ya bayar wajen ciyar da ma’akatar lafiyan jihar gaba cikin kusan shekaru biyu da gwamnatin mai ci, dama shekaru da yayi a gwamnatin daya gabata.

Gwamnan Zulum ya kuma umarci shugaban ma’aikata farfesa Isa Hussani Marte da rike mukamin kafin nada kwamishia daya dace.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply