Gwamna Zulum Ya Roki Gwamatin Tarayya Data Karo Jami’an Tsaro Dama Kayan Aiki Don Yaki Da Ta’adanci A Jihar Borno.

zulum (16)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum ya bukaci gwamnatin tarayya data karo jamian tsaro da kayan yaki don cigaba da yaki day an kungiyar Boko Haram.

Gwamna Zulum ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa da gidan talabijin na Channels a shirin su na Politics Today.
Acewarsa har yanzu akwai wasu manyan gurare 3 dake hannun yan kungiyar kuma jamian sun kasa kawo karshen yakin day a dade.

Zulum yace yankin tafkin Chadi, dajin Sambisa da dutsen Mandara dake karamar hukumar Gwoza na cikin guraren da suke zama kuma suna kai hari suna komawa wajen.

Haka nan yace idan gwamnati nason yaki day an taaddan yak are sai ta hada da jamian soji kasashen dake makotaka da ita na Nijar, Chadi da Kamaru.

San nan yace jirgin sojin saman Najeriyar yayi matukar kokari wajen tarwatsa gurare da dama yayin ayyukan da suke gudanarwa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply