
Gwamna Babagana Umara Zulum ya karbi bakuncin takwaransa na jihar Kwara Abdulrahman Abdurrazaq a fadar gwamnatin jihar dake Maiduguri.
Gwamnan na jihar Kwara ya kawo ziyarar Maiduguri don yin jaje ga gwamnan jihar Babagana Umara Zulum dama dukkkanin yan jihar ta Borno kan kisan manoma fiye da 60 a kauyen Zabarmari.
Gwamnan kwaran ya samu rakiyar Sanata Ibrahim Yahya, Sanata Lola Ashiru, Sanata Sadiq Umar da mai bada shawara kan al’amuran siyasa Sa’adu Salahu.

