Gwamna Zulum Ya Kai Ziyara Dikwa Ya Raba Naira Miliyan 115 Da Abinci Ga Mutane 34,000

zulum (20)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By:Ndahi Marama, and Hadiza Garba Maiduguri
Gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci garin Dikwa ranar Alhamis inda ya duba yadda akayi rabon kudade da kayan abinci gay an gudun hijira 34,000maza da mata.

23,000 daga cikin matan sun samu N5,000 wanda ya kama Naira miliyan 115 sai kuma mazan su 11,000 da kowane magidanci ya samu buhun shinkafa, wake, masara da kuma man girki.

Rabon na karkashin tsarin da kokarin gwamnatin jihar wajen taimakawa masu karamin karfi wadanda rikicin Boko Haram ya shafi hanyoyin neman abincinsu da kuma kare mutane yankin daga shiga kungiyar ta Boko Haram.

Haka nan gwamna Zulum bayan rabon kayan agajin ya ziyarci babban asibitin na Dikwa dama makarantar firamaren ta Dikwa.

Haka nan ya bada umarnin a duba lafiyar yan kungiyar sa kai 9 da suka sambayan harin day an kungiyar Boko Haram suka kai garin na Dikwa da kuma umarnin fitar dasu kasashen waje idan likitocin sun bada umarnin hakan.

Dandal Kura Radio International ta gano cewa wadanda suka samu raunin na cikin dubban wadanda ke taimakawa jami’an soji wajen yaki day an ta’addan na Boko Haram inda wasu ma suka rasa kafafunsu suka zama guragu..

Kafin nan gwamnan ya kara kudaden yan kungiyar sa kan da kashi 100 da kuma kari gay an sa kai 9 don habbaka rayuwarsu.

Ndahi Marama ya rawaito cewa gwamna Zulum ya taimakawa yan gudun hijirar donrage musu radadin da suke ciki da kawo karshen hare-haren Boko.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply