Gwamna Zulum Ya Kaddamar Da Ginin Makarantar Jami’a Mai Zaman Kanta A Jihar Borno

zulum (3)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwaman jihar Borno Babagana Umara Zulum a jiya litinin ya kaddamar da ginin jami’a mai zaman kanta da za’ayi na AL-Ansar anan birnin Maiduguri.

A watannin baya gwamnan ya amince da fili mai hecta dari ga gidauniyar Al-Ansar da take gina jami’ar, wanda shugaban kungiyar kuma wanda ya samar Dr Muhammad Kyari Dikwa, tsohon jami’in gwamnati ke jagoranta.

Yayin jawabin, gwamna Zulum yabada umarnin shimfide kwalta mai tsawon kilomita 2.3 cikin sabuwar jami’ar tare kuma da burtssan ruwa .

Haka kuma ya umarci ma’aikatar manyan makarantun ilimi dana kimiyya da fasaha dama kirkira cewa su hada kai da sabuwar jama’iar domin gano hanyoyi da gwamnatin jiha zata iya bada gudumawarta cikin aikin.

Haka zalika gwamna Zulum yayi alkawarin bada goyon baya makamanci hakan ga duk wanda yake da burin saka jari a jihar Borno musamman ma bangaren ilimi.

Shugaban gidauniyar Al-Ansar kuma wanda ya samar da jami’ar Mohammed Kyari Dikwa ya mika godiyar sag a gwamna Babagana Umara Zulum bisa goyon baya daya bayar a samar da jami’ar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply