Gwamna Zulum Ya Jagoranci Rantsar Da zababbu Shugabannin Kananan Hukumomi 27.

ZULUM-INAUGURATE-COMIITE
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Laraba ya jagoranci rantsar da zababbun shugabannin kananan hukumomi 27, daga cikinsu, akwai malaman jamioi biyu masu rike da digiri na uku.

Malaman biyu sune Farfesa Adamu Alooma, dake a fannin hada-hadar kudi, wanda kuma tsohon Dean, fannin management sciences a Jamiar Maiduguri, wanda ya yi rantsuwa ya zama shugaban karamar hukumar Damboa.

sannan akwai Farfesa, Ibrahim Bulama na jami yar Maiduguri wanda yayi rantsar a matsayin shugaban karamar hukumar Gwoza.
Dukkanin Farfesan sun halarci zaben shugabancin karamar hukumar da kuma kansiloli da aka gudanar a ranar 28 ga Nuwamba.
A lokacin rantsarwar, wanda ya gudana a dakin taro dake gidan gwamnati a Maiduguri, Gwamna Zulum ya baiyana cewa ba a gudanar da zabe a jihar borno ba, sama da shekaru 10, saboda matsalar tsaro da da ake fuskanta a jihar .

Bikin ya samu halartar manyan shugabannin jamiyyar APC karkashin jagorancin tsohon gwamna Kashim Shettima, shugaban riko na jamiyyar APC Ali Bukar Dalori, da sauran mambobin majalisar kasa da na jiha karkashin jagorancin kakakin majalisar, mambobin majalisar zartarwar jihar, dattawan jamiyyar, sarakunan gargajiya da dai sauransu.

Gwamnan ya taya dukkan zababbun shugabannin kananan hukumomin murna tare da tunatar da su babban aikin da ya rataya a wuyansu
A jawabinsa, Gwamna Zulum ya umarci ma’aikatar kananan hukumomi da masarauta da ta hanzarta sakin duk kudaden da aka ware wa kananan hukumomi 27 daga asusun tarayya ga zababbun shugabannin domin su fara gudanar da aiyukan yanda ya kamata

A karshe gwaman ya yi kira ga zababbun shuwagabannin da suji sauron tsoron Allah, aduk abubuwan da suke tare da sauke nauyin da ke kansu

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply