
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya fadada hanin bangar siyasa zuwa karamar hukumar Gwoza.
Gwamnan ya bayyana hakan yayin da yakai ziyara fadar sarkin Gwoza yayin day a kai ziyarar aiki karamar hukumar.
Haka nan gwamnan ya bayyana rashin jin dadinsa na yadda matasan ke gudanar da bangar siyasar inda ya bukaci yan siyasar dake daukar nauyinsu su dasu kauracewa wan nan aikin.

Yace gwamnatin ta fara samar da ayyukan dad a za’a koyawa matasan aiki da sana’oi don su zama mutane na gari cikin al’umma.
Haka nan yace bai ji dadin yadda yaga matasan ba dauke da pastar yan siyasa shuna ihu suna cin zarafin jama’a.
San nan yace zasu yi iyakar kokarinsu wajen ganin matasan basa shiga cikin bangar siyasa.
Haka nan yace bazai taimakawa ko wane dan siyasa da yake lalata rayuwar matasa ba.
San nan ya umarci hukumomin tsaro dasu kama duk wanda aka gay an yawo da sunan bangar
