Gwamna Zulum Ya Gana Da Ministan Wutar Lantarki Game Da Rashin Wuta A Maiduguri

ZULUM
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

ranar Alhamis daya gabata ne gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci ministan wutar lantarki Engr.

Saleh Mamman a Abuja domin tattaunawa game da batun gyarar layukan wutar lantarki a babban hanyar Maiduguri zuwa Damaturu da yan Boko Haram suka lalata.

Wutar wanda aka aka lalata da nakiya yabar jama’ar Maiduguri cikin duhu kusan wata daya kenan, wandaaikin gyarar ya sake komawa baya sakamakon layukan wutan yankin biyu sun kara samun matsala.

Gwamna Zulum ya nemi taimakon gwamnati tarayya da ta samar da na’urar wuta mai amfani da rana na solar da tashoshin su a biranai da kauyukan jihar Borno. 

Haka zalika gwamna Zulum ya kuma nemi gwamnati ta sa hankali kan ayyukan makamashin wuta na Mambila dana Dadin Kowa na jihohin Taraba da Gombe, tare da cewa ayyukan biyu suna da tasiri warware matsalolin tattalin arziki da yake fuskantar yankin arewa ta hanyar farfado da kanana da manyan sana’o’i.

Ministan lantarkin, Engr. Mamman yaba da tabbacin cewa duk da matsalolin da suke kasa, za’a kammala ayyukan gyaran lantarkin jiha cikin kankanin lokaci kuma ya bayyana cewa tuni ma’aikatar lantarki ta zabi yankunan da zayi ayyukan wutar solar ciki harda jihar Bornon sannan ya godewa gwamna Zulum bisa ziyarar daya kai masa kuma ya yabi irin salon shugabancin sa da cewa gwamnatin al’umma ne.

Daraktan ma’aikatar Engr. Faruk Yabo Yusuf hade dana kamfanin wuta na TCN Engr. Sule Ahmed Abdulaziz, sun bayyana wa gwamna Zulum yadda sabbin ayyukan wutar zata kasance a jiha.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply