Gwamna Zulum ya dauki aniyar sake bude gonnakin dake hanyar Molai-Dalwa

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Lahadi ya ziyarci al’ummomin Mulai da Dalwa sannan kuma ya gana da jami’an tsaro don fara hanyoyin sake bude filayen noma a wannan layin, ta yadda za a kauce wa matsalar rayuwa.

Zulum ya yanke shawarar ne bisa ga umarnin da shugaban kasa Buhari ya baiwa sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro na ranar Alhamis da su yi aiki tare da Gwamnatin jihar Borno sannan su zo da wasu dabaru da zasu baiwa mutane damar shiga gonakin su.

Shugaba Buhari yayin ziyarar ta kwana daya da ya kai a Borno ya ya umarci Kwamandan Theater na Operation Hadin Kai da sauran jami’an tsaro da su yi aiki da hanyoyin tare da Gwamnatin Jihar Borno da kungiyoyin manoma, kan hanyoyin kara samar da hanyoyin da manoma za su samu lafiya gonakinsu, dazuzzuka da wuraren kamun kifi.

Gwamna Zulum ya je zuwa Dalwa, Konduga sannan daga bisani ya koma Ngwom a karamar hukumar Mafa.

Ya kuma tantance filayen noma ya kuma tattauna da yi hulda da jami’an tsaro gabanin sake dawo da ayyukan noma.

Ya kuma ce zai kafa wata gonar kashin kansa a wannan yankin inda zai dinga ziyartar a ranakun da ba na aiki ba.

Zulum yayin da yake jawabi ga dubban mazauna Molai da ke kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damboa ya yi kira ga manoma su ci gaba da harkokin su na noma lafiya daga gobe.

A Molai, Zulum ya kuma duba aikin gidaje 500 na sake tsugunar da jama’a. Gwamnan ya nuna rashin gamsuwa kan ingancin aiki.