Gwamna Zulum Ya Dakatar Da Ziyarar Da Zaikai Birnin Tarayya, Yayin Daya Ziyarci Yankuna 4 A Karamar Hukumar Hawul.

zulum (20)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

ranar lahadi ne gwamna BG Zulum ya bar birnin tarayya Abuja zuwa Maiduguri domin ziyartar yankunan day an kungiyar BH suka kai hari a ranar asabar da yamma a karamar hukumar Hawul dake kudancin jihar nan.

Gwamnan wanda ya tashi daga Maiduguri zuwa Katsina zuwa Abuja a ranar alhamis domin wasu ayyuka. Ya dakatar da ziyarar bayan harin da aka kai kudancin jihar nan.

Yankuna 4 ne harin ya shafa da suka hada da Tashan Alade, Shafa, Azare da Sabon-Kasuwa inda suka lalata makarantu, shaguna da wuraren ibada, sannan an kashe mutane 3 a Shafa da suka hada da maharba 2 da jami’in sa kai 1, haka kuma sun sace dubban buhuhu nan anfanin gona da aka girba kwanan nan.

Gwamnan ya duba wuraren da aka lalata a Yimirshika, Azare,Sabon-Kasuwa da kuma Shafa kuma yayi umurnin gaggauta gyara wuraren da suka hada da ofishin yan sanda da kasuwa da sauran su.

A Shafa gwamna Zulum ya bada motocin sintiri guda 6 da wasu kayaki domin inganta tsaro a yankin haka ma a Yimirshika ya bada motoci ga maharba da jami’an sa kai.

Daga karshe gwamnan yayi jawabi ga mazauna yankin da suka koma garin Yimirshika bayan an dakatar da harin da yan ta’adda suka shirya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply