
Gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum ya dakatar da yan bangar siyasa da akafi sani da ECOMOG a dukkan bangarori a karamar hukumar Bi una jihar.
Ya bayyana haka yayin kaddamar da masallaci a Biu, kuma ya bada bashi ga kungiyar yan kasuwa daga kananan hukumomin Biu, Gwoza da kuma Maiduguri.
Yace karamar hukumar Biu na komawa baya sakamakon yan bangar siyasa dalilin haka ya dakatar da su.

Yace gwamnatin jihar Borno zata farfado da madatsan ruwa domin noman ban ruwa ga manoma da kuma samar da ayyuka ga matasa.
