Gwamna Zulum ya bukaci shuwagabannin gargajiya da su kiyaye al’adun gargajiya.

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi kira ga shugabannin gargajiya da na addini da su tashi tsaye wajen zaburar da al’ummarsu musamman matasa wajen kiyaye ka’idojinsu da dabi’unsu.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen bikin ranar al’adun Bura na shekarar 2022 da kungiyar ci gaban al’ummar Marama ta shirya wanda ya gudana a makarantar Sakandaren Gwamnati ta Marama Play Ground dake karamar hukumar Hawul ta jihar.

Gwamnan wanda mataimakinsa Usman Kadafur ya wakilta, ya ce ranar al’adun Bura ta 2022 mai taken “Echoes of a Dying Culture.
Gwamna Zulum ya yi kira ga al’umma da su ci gaba zuwa makarantu domin ilimi ya kasance ginshikin ci gaba a kowace al’umma, tare da tabbatar wa al’umma karin ayyukan ci gaba kafin karshen mulki sa.

Mai martaba Sarkin Biu, Mai Mustapha Umar Mustapha ya yabawa wadanda suka shirya wannan biki da daukacin ‘ya’yan masarautar Biu maza da mata bisa hadin kai da fahimtar juna wajen kiyaye da farfado da al’adunsu.

Mai martaban ya kuma yi addu’ar Allah ya ci gaba da hada su domin ci gaba da ci gaban al’ummarsu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Related stories

Leave a Reply