
From: Hadiza Garba, Maiduguri
Gwamna Babagana Umara Zulum yace duk da abubuwan da yake faruwa na kwanan nan, ana samun nasara da cigaba na yanayin tsaro a jihar nan dama yankin arewa maso gabas a gwamnatin shugaba Buhari.
Gwamna Zulum ya bayyana haka yayin jawabi ga kungiyar dattawan arewa a nan Maiduguri.
Gwamnan yace daga kididdiga na al’amuran kananan hukumomi 27 na jihar nan da aka fitar tun shekarar 2011, yace duk da abubuwan da suke ta faruwa a jihar nan ana samun cigaba a jihar nan da yankin arewa maso gabas karkashin shugabancin shugaba Buhari.

Yace idan za a iya tunawa shekaru da dama da suka wuce kananan hukumomi da dama a jihar nan ba a iya zuwa, amma yanzu ana sarakunan gargajiya na jagorantar su kamar kananan hukumomin Bama, Gwoza, Askira-Uba, Dikwa, Ngala, Monguno, Kukawa, Damboa, Konduga, Mafa wanda duk a baya ba a iya zuwa ko a zauna a ciki.
Kuma a lokacin ne ake samun tashin bama bamai da harbe harbe a yankuna da daman a fadin Maiduguri, amma hakan ya tsaya karkashin shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Yace a yanzu yafi damuwa da abubuwan da yake faruwa a yankin akan ya alakanta shi da abinda ya wuce.
