Gwamna Zulum Ya Bayyana Cewa An Ssamu Nasara A Tafiyarsa Abuja

zulum (16)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana ziyarar da yayi ta aiki zuwa Abuja a matsayin wadda aka samu nasara.

Gwamnan ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai bayan ya dawo a filin saukar jirage dake birnin Maiduguri.

Wasu daga cikin ayyukan da gwamna Babagana Umara Zulum ya gudanar a Abuja sun hada da ziyarar day a kaiwa Ministan Ilimi Mallam Adamu Adamu bayan umarnin da aka bayar na kafa babbar makarantar gwamnatin tarayya dake monguno inda Ministan ya kara bayyana wa cewa zasu kafa wata a babbar makarantar ilimin a kudancin jihar Borno.

Haka nan gwamnan yace ayyukan biyu da aka amincewa jihar abun ayi murna ne kuma ziyarar day a kai hukumar daukar ma’aikata ta kasar tace zata bada gurabe na musamman gay an asalin jihar ta Bormo.

Daga filin saukar jirage gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ya wuce zuwa babban ofishin kula da motocin Borno Express inda ya duba sababbin motocin da gwamnatin ta samar guda 80 wadanda za’a dinga zirga-zirga dasu a cikin gari dama doguwar tafiya don bunkasa harkar sufuri a jihar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply