Gwamna Zulum, Da Makarabansa Sun Halarci Jana’izar Shehu Dikwa A Birnin Maiduguri

ZULUM-INAUGURATE-COMIITE
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

From Babagana Bukar Wakil Ngala, Maiduguri
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, Shehun Borno, Abubakar Umar Garbai El-Kanemi, da sauran sarakunan gargajiya, da manyan jamian gwamnati sun halarci sallar janaizar marigayi Shehu Dikwa, Mohammed Ibn Masta na II.

Limamin Idaini na Borno, Imam Shettima Mamman Saleh ne ya jagoranci sallar janaizar a Fadar Shehun Borno dake Maiduguri.

Shehu Mohammed Ibn Masta II ya rasu a ranar Asabar birin taraiya Abuja bayan yasha fama da rashin lafiya Ya rasu yana da shekara 75 a duniya .

A yayin da yake zatawa da manema labarai bayan sallar janaizar Gwamna zulum ya bayyana mutuwar a matsayin babban rashi.

Sannan ya yi addua Allah Madaukaki sarki ya yi masa rahama ,ya sa shi a Jannatul Firdaus.

Shima a nasa jawabin Shehun Borno, Abubakar Umar Garbai El-Kanemi ya bayyana rasuwar marigayi a matsayin babban rashi ga daukacin mutanen Borno.
Sannna ya yi masa adua Allah Madaukakin Sarki ya sashi a Jannatul

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply