Gwamna Zulum Ya Kai Ziyara Ga Yan Gudun Hijiran Jihar Borno Dake Kasar Chadi.

ZULUM
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnnan jihar Borno Ferfesa, Babagana Umara Zulum ya kai ziyara kasar chadi domin duba yan Hijiran jihar Borno dake matsugunnin yan gudun hijra na Darsalam dake Baga sola dake kasar chadi.
Gwamanan kasar chadi Fadul Tijjani shine ya karbi bakancin gwamnan.

Gwamnnan zullum ya kuma gana da masu lura da yan hijiran domin jin matsalolin da suke fuskanta da kuma yin nazari akan hanyar da ya dace a shawo kan matsalolin.

Gwamnan kuma ya jagoranci rarraba kudi wanda ya kai kimanin naira miliyan hamsin ga yan gudun hijira dubu biyar inda kowane magidanci ya tashi da naira dubu goma.

Bayan nan kuma Gwamnan ya wuce N’Djamena, babban birnin chadi domin duba sauran yan gudun Hijira dake wajen.

Cikin wadan da suka yi rakiyan gwamnnan sun hada da mamba mai wakiltan kukawa Haruna Kukawa, kwamishinan harkar gargajiya Sugun Mai Mele, mataimakin gwamnan a kan muhalli Zanna Jabu tare da shugaban kamfanin robobi na borno plastic Abatcha Jarawa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply