Gwamna Fintiri Yayi Allah Wadai Da Harin Da Yan Boko Haram Suka Kai Garin Garkida .

fintiri 2
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri yayi Allah wadai da harin da yan kungiyar Boko Haram suka kai garin Garkida dake karamar hukumar Gombi a jihar Adamawa.

Hakkan na kunshe a cikin sanarwar da maitaimakin Gwamna a bangaren yada labarai Humwashi Wonosikou ya bayar.
Wani dan gani da ido ya bayyan cewa yan kungiyar Boko Haram din sun kawo harin ne a ranar alhamis da ya gabata tare da kashe mutane biyu.

Fintiri Ya bayyana cewa wannan harin farune sakamakon takurar da yan ta’addan suke ciki sakamakon yakarsu da sojoji sukeyi.

Gwamnnan ya jajantawa mazauna garin Garkida kuma yayi kira ga jami’an tsaro da su kara kaimi a yaki da yan ta’ada da suke yi a cikin jihar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply