By Hassan Umar shallpella, Adamawa
Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya jaddada kokarin gwamnatinsa na kare rayuwar mutane da dukiyoyinsuda harkar tsaro data addabi wasu sassa na kasar.
Gwamnan ya bayyana hakan yayin gabatar da lakca da aka shirya ta azumin Ramadan wanda Centre for Islamic Thought ta shirya a Yola wanda akayi a babbar kwalejin ilimi ta Yola inda yace gwamnati zata cigaba da yaki da ta’addanci a cikin al’ummma.
babban mai bashi shawara kan harkokin adddinin Islama Ustaz Ali Mamman ne ya wakilce shi inda yace gwamnatin ta fara yaki da yan kungiyar nan da ake kira Shillaa fadin jihar.
Fintiri sya bayyana cewa kullum gwamnati na sauraron sakonnin daga shugabannin addinai inda suke kira da acigaba da yi musu addu’ar tafi da gwamnatin yadda ya dace.
a nashijawabin shugaban cibiyar Dr. Usman Ahmed Dadah yace cibiyar na gudanar da ayyukan Da’awa ta hanyar koyarwar kur’ani da sunna.
Dadah yace suna gudanar da ayyukan kalandar musulinci, lakcocin Ramadan daukar nauyi abubuwan musulinci da sauran ayyukan musulinci.