Gwamna Buni Ya Yabawa Dakarun Sojoji, Sanna Yayi Alkawarin Basu Goyon Baya.

yobe2
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yabawa dakarun sojojin Operation Lafiya Dole kan namijin kokari da sukeyi na maido da zaman lafiya da tsaro a jihar da kuma Arewa maso Gabas baki daya.

Buni ya yi wannan yabo ne a ranar Jumaa a wajen bikin cin abincin kirsimetin da shugaban hafsin sojan kasa, Laftana-Janar. Tukur Buratai, ya shirya a makarantar Sojoji ta Musamman dake Bunu Yadi.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Idi Gubana, ya ce yanayin tsaro a jihar ya bunkasa sosai a yan kwanakin nan, saboda jajircewar sojoji da sauran jami’an tsaro.

A cewarsa kokarin da sojojin keyi na ganin an kawo karshen asaran rayuka da dukiyoyin jama;a. Yace sojojin sun samu tallafi da goyon baya daga gwamnati domin su cigaba da ayyukansu yanda ya kamata .
A nasa jawabin, Shugaban hafsin sojojin laftanan ,Yusuf Tukur Buratai ya ce bikin sun shirya ta ne domin bawa sojojin kwarin gwaiwa a yakin da suke yi da yan taada.

Buratai ya tabbatarwa da sojojin cewa babban hafsan sojan zai cigaba da dasu goyan baya da abubuwan da suke bukata domin gudanar da ayyukan kaman sauran kasashen duniya.

A karshe ya bukaci sojojin da suyi addua ga sojojin da suka kwanta dama a yayin gudanar da ayyukansu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply