Gwamna Babagana Umara Zulum Ya Raba Goron Kirismeti Ga Sojoji Sama Da Dari 7.

zulum (6)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

A jiya Talata ne gwamna Babagana Umara Zulum ya ziyarci shalkwatar bataliyan sojoji na 151 a garin Bama, tare da bada goron kirismeti ga sojoji sama da dari 7.

Gwamnan yayi ganawar sirri da kwamandan birget na 21 birgediya janar Waheed Shaibu da kuma kwamandan dake jagorantar bataliya na 151 manjo A A Umar bayan yayi jawabi ga dakarun.

Yace yana daukan kowa dai dai ne da kuma bisa cancanta, haka kuma ya gano irin kalubalen da jihar nan take fuskanta a wasu yankunan wanda hakan ba zai hana bayyana nasarorin da ake samu ba a wasu yankin.

Ya bayyana bataliya na 151 a cikin wadan da suka samu nasarori a jihar sakamakon samun nasara da suke akan yan kungiyar BH tun bayan kafuwar su.

Gwamna Zulum ya yaba da kokarin su da kuma jajircewar su kuma yayi addu’an Allah ya da da kare su da sauran hukumomin tsaro baki daya.

Haka kuma gwamnan ya duba kauyen Gurusoye dake bayan shalkwatan bataliya na 151 wanda yan kungiyar BH suka lalata, ya bada umurnin gina sabbin gidaje dari 2domin sake matsugunai tare da samar da wuraren da zai janyo hankalin jama’a ta fuskar farfado da tattalin arziki.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply