Gwamna Abubakar Bello Ya Bada Umurnin A Rufe Makarantun Kwana A Jihar Naija.

Niger State
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Akalla dalibai 27 ne da ma’aikata 3 da kuma mambobi 12 aka sace a safiya ranar Laraba a makarantar gwamnatin na kimmiya dake Kagara a karamar hukumar Rafi na jihar Naija.

Gwamnan jihar Abubakar Bello ya bada umurnin gaggawa na rufe makarantun kwana a yankunan da yan bindiga ke barna na har sai baba ya gani.

Dandal Kura ta rawaito cewa yawancin makarantun da abin yafi shafa sune a kananan hukumomin Rafi, Mariga, Munya, da kuma Shiroro.

Gwamnan ya bada wannan umurnin ne yayin da yake Magana da manema labarai bayan faruwar lamarin inda yace an kashe daya daga cikin daliban mai suna Benjamin Doma a cikin harin.

Haka kuma ya tabbatar da faifan bidiyon da ya zaga gari wanda yan bindigar ke farin cikin garkuwa da matafiya da sukayi a ranar Lahadi inda suka bukaci naira miliyan dari 5 na kudin fansa.

Gwamnan yace ba tsarin gwamnati bane na biyan kudin fansa, yace ko an biya ma yan bindigar zasuyi amfani da kudin ne wajen siyan makamai.

Daga karshe yace gwamnati ta damu matuka kan abinda yake faruwa a jihar wanda a yanzu ya zama a bayyane.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply