Gidauniyar UNICEF ta Koka kan Matsalar Tamuwa a Arewa-Maso Gabashin Najeriya

UNICEF-small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gidauniyar majalisar dinkin duniya mai kula da yara wato UNICEF ta bayyana cewa akwai tsananin rashin abinci mai inganci arewa maso gabashin najeriya, inda kimanin yara 88,000 ke cikin hatsarin ciwon da zai iya sa su rasa rayukansu a yankin. Kuma har yau ba’ayi musu magani ba.

UNICEF ta kara da cewa akwai kimanin yara miliyan 1 daga shekara 6 zuwa wata 59 a jihohin 3 da ke fama da rikicin ta’addanci wato Adamawa, Borno da Yobe dake fama da ciwon.

Yayin da yake Magana a taron da suka gudanar a Maiduguri na kwana 5 Geoffrey Ijumba, yace acikin ko wane yara 5 cikin 440,000 masu fama da ciwon na cikin mummunan hadari da zai iya sawa su rasa rayukansu.

Ya kara da cewa mata masu juna biyu da masu shayarwa 230,000 ma na fama da matsalar a yankin na karancin abinci mai inganci.

Haka nan yace ingantaccen abinci shine ke gina jikin yaro da lafiyarsa a kowace kasa. Har ila yau Ijumba ya kirayi mutane 32 da suka halarci taron dasu taimaka wajen bada tasu gudunmawar ga yara.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply