Gidauniyar Jonathan Ta Bukaci Aiki Jaridanci Mai Sahihanci

Gidauniyar Goodluck Jonathan tayi kira ga gwamnatocin afirka dasu tabbatar da yancin furucin yan jarida a kasashen su kuma ya bukaci yan jaridar dasu dauki aikin su wani dama na ci gaban kasa.

Gidauniyar tay kiran ne ta jami’in sadarwarta Mr Wealth Ominabo , kuma yace hakika Afirka zatafi ci gaba idan anyi amfani da bayanai matsayin abu naci gaba ba wani makami na haddasa rarrabuwar kawuna ba

Yace daraktar gidauniyar Miss Ann Iyonu, tace ungiyar su tana tabbatar da cewa jama’a tare da gwamnatoci sunyi amfani da bayanan sahihanci wajen aiwatar da gaskiya, zaman lafiya, tsaro dama ci gaba.

Haka zalika gidauniyar ta sake jaddada yan jarida da kasancewa abokan ci gaba kuma ta nemi al’umma da sauran masu ruwa da tsaki data basu girma duba da irin ayyuka da sukeyi.