Fiye Da Yara 22,000 Ne Ke Kamuwa Da Cuta mai Karya Garkuwar Jiki A Najeriya

majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa fiye da yara 22,000 ne ke kamuwa da cuta mai karya garkuwar jiki a Najeriya duk shekara.

majalisar ta bayyana hakan ranar Talata a taron wayar da kai na kare yaran kamuwa daga iyayensu mata wanda a turance ake kira vertical transmission.

yayin da yake Magana a madadi majalisar Mr Claes Johansson, shugaban hada rahotannin na majalisar ta fannin kula da kudaden kananan yara wato UNICEF yace anyi taron ne don hana yaduwar daga iyayen zuwa yaransu.

yace zasuyi aikin da zasu dakile cutar cikin shekaru 5, inda suka ce hakan zai kawo karshen annobar.

darakta Janaral na hukumar masu kula da cutar Dr Gambo Aliyu, hakn yafi kan ace za’a dakile yaduwar cutar daga uwa zuwa danta,.

ya kuma bayyana cewa a shekarar 2016 akwai mata masu ciki 13,000 dake dauke da cutar kuma basa shan magani.