Farashin Litan Man Fetur Ya Haura Naira 175 A Maiduguri

borno-state-small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Farashin litar man fetur ya tashi daga naira 162 zuwa tsakanin naira 170 da 175 a birnin Maiduguri da kewaye.

Haka kuma kungiyar yan kasuwan man fetur a Najeriya IPMAN ta alakan ta karancin man fetur ga matattarar man gundumar yankin, wanda an samu hawar farashi duk da tabbaci da NNPC ta bayar na cewa babu batun Karin farashin man fetur.

Wani ma’aikacin gidan mai Chiroma Kadai, yace man sun yanke a tankokin su kuma NNPC bata sayar wa, kuma ya danganta karuwar farashin sabili da karancin sa, sannan yayi kira ga NNPC data samar da mafita ga karancin.

Da yake wa wakilin mun bayani, daya daga cikin manyan mabobin kungiyar IPMAN ne yaba da tabbacin sabon farashin da aka sanya na man, wanda yace an samu karuwar kudin sufurin man daga naira 149 zuwa 163 kuma ya alakanta karancin da hakan sannan yace yan kasuwa suna amfani ne kadai da banbance-banbancen farashi.

Kungiyar IPMAN ta kuma roki NNPC da ta tabbatavan samu isasshen mai domin mambobin ta suna sayan man ne a mattara kan naira 164, kuma su biya naira daya ga ko wani zubi hade da biyan naira shida na sufurin ko wani lita daya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply