Fadar Shugaban Kasa Taja Hankalin Gwamnan Jihar Ond

buhari
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Fadar shugaban kasa taja hankalin gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu daya kula da hanyoyin magance ayyukan bata gari a jihar sa domin gujewa sabawa dokar kasa.

Hakan yana kunshe cikin sanarwa da Mallam Garba Shehu, mataimakin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai ya fitar a Abuja

Gidan rediyo Dandal Kura ta ruwaito cewa sanarwar ya biyo bayan umarrni da gwamnan na Ondo ya bayar na cewa dukkan makiyaya dake jejin jihar suyi kaura kuma ya basu kwanaki 7 su dakatar da kiwo.

Bayanan tsaron na nuna cewa muddin gwamna Akeredolu ya aiwatar da hakan to ya sabawa doka kuma ta takalo rashin tsaro wanda tuni shugaban kasa yasha alwashin kare kundin doka a kasa kuma yaba da misali da kungiyar Biafara da kuma na Muslim Solidarity Forum a Sokoto da cewa bai basu damar cin zarafin ko wani dan kasa ba sannan a shirye yake yayi amfani da tanade-tanaden doka domin kare al’umma da kuma tabbatar da damar ko wani dan najeriya na zama a inda yaso ko domin adalci.

Sanarwar ya kuma kara da cewa dole gwamnatin jihar Ondo da sauran jihohi 35 na Najeriya su raba tsakanin bata gari da kuma jama’a masu amfani da doka wanda yace yakar ayyukan bata gari na nufin girmama jama’a domin muhimmancin hakan a kasar nan.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply